1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Gasar zakarun Turai da fatan Jamusawa

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 8, 2024

Kungiyar Borussia Dortmund ta Jamus ta yi nasara a kan takwararta ta Paris Saint-Germain ta Faransa a wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai Champions League, lamarin da ya ba ta damar zuwa wasan karshe.

https://p.dw.com/p/4fdCj
Jamus | Borussia Dortmund | Faransa | Paris Saint-Germain | Gasar zakarun Turai
Borussia Dortmund ta yi wa Paris Saint-Germain yankaan kauna a gasar zakarun TuraiHoto: Robert Michael/dpa/picture alliance

In har Borussia Dortmund ta samu nasarar a wasan karshe na gasar Champions League da za a fafata a ranar daya ga watan Yunin da ke tafe a Ingila kana ta karkare gasar Bundesliga a matsayi na biyar da take a yanzu, to hakan zai bai wa kungiyoyin Eintracht Frankfurt da SC Freiburg da TSG Hoffenheim da kuma FC Augsburg da ke a matsayi na shida da na bakwai da na takwas da kuma na tara damar fafatawa a manyan wasannin kwallon kafa na Turai a kakar wasannin ta badi.