1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Joe Biden da Donald Trump na yakin neman zabe a Georgia

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 9, 2024

A ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka

https://p.dw.com/p/4dKzm
Hoto: ABACA/IMAGO;AP Photo/picture alliance

A Asabar din nan shugaban Amurka Joe Biden da kuma tsohon shugaban kasar Donald Trump za su kaddamar da yakin neman zabe a jihar Georgia mai matukar tasiri a siyasar Amurka.

Karin bayani:Biden ya caccaki Donald Trump

Wannan dai shi ne karon farko a bana kenan da za a ga fuskokin shugabannin biyu suna yakin neman zabe a jiha daya, bayan da suka jima suna zargar juna da gurgunta Dimokuradiyya.

Karin bayani:Biden da Trump sun yi fintinkau a "Super Tuesday"

A ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka, inda jam'iyya mai mulkin kasar ta Democrats ta tsayar da shugaba mai ci Joe Bide, yayin da Donald Trump ke zama mai neman takara tilo daga jam'iyyar hamayya ta Republican, bayan janyewar abokiyar hamayyarsa Nikki Haley.