1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada ta kori jami'in diflomasiyyar Indiya

Abdourahamane Hassane
September 19, 2023

Kanada ta kori wani babban jami'in diflomasiyyar Indiya tana mai cewa akwai shaidu da ke nuna cewa Indiya ce ke da alhakin kashe wani shugaban mabiya addinin Sikh a yammacin Kanada a watan Yuni, da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4WV2a
Singh Nijjar
Singh Nijjar Hoto: Ethan Cairns/The Canadian Press/AP/picture alliance

A cikin wani jawabi da yayi a majalisar dokokifiraministan Kanada Justin Trudeau ya ba da haske game da kasancewartabbatacciyar shaida da ke nuna cewar wakilin gwamnatin Indiya  na da hannu a kisan Hardeep Singh Nijjar, dan kasar Kanada mai asilin indiya ga dai abinda yake cewa: ''Duk wani hannu da wata gwamnatin waje ta sa wajen kashe wani dan kasar Kanada a Kanada cin zarafi ne da ba za a amince da shi ba.'' Hardeep Nijjar mai fafutukar ganin an kafa kasar Sikh da aka fi sani da Khalistan,hukumomin Indiya na nemansa ruwa jallo bisa zarginsa daaikata ta'addanci da hada baki na kisan kai.