1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarima Harry da mai dakinsa sun kammala ziyara a Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AMA/MNA
May 13, 2024

Dalilin ziyarar dai shi ne don ganawa da sojojin Najeriya da ma sauran masu damara da suka samu raunuka yayin aiki.

https://p.dw.com/p/4fm1q
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Yarima Harry da mai dakinsa Meghan sun kammala ziyarar kwanaki uku a Najeriya, bayan da suka ziyarci Abuja babban birnin kasar, sai Kaduna, sannan suka karkare da Lagos.

Karin bayani:Yarima Harry a kotu kan rashin tsaro

A yayin ziyarar, Yarima Harry da Gimbiya Meghan sun ziyarci wata makaranta a Abuja da ta gudanar da taro kan kula da lafiyar kwakwalwa, sai wasan kwallon kwando a Lagos.

Karin bayani:Auren Yarima Harry da Gimbiya Meghan

Dalilin ziyarar dai shi ne don ganawa da sojojin Najeriya da ma sauran masu damara da suka samu raunuka a lokacin da suke tsaka da aiki, da nufin karfafa musu gwiwa, tare da kara tallata gasar wasa da ya kirkiro mai suna Invictus Games, da ke agaza musu da kuma 'yan mazan jiya.