1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Kenya: Zaman makoki saboda ambaliyar ruwa

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 8, 2024

Shugaba William Ruto na Kenya ya ayyana ranar Jumma'ar da ke tafe a matsayin ranar hutu, domin yin zaman makoki na mutane 238 da suka rasa rayukansu a mummunar ambaliyar ruwan da kasar ta tsinci kanta a ciki.

https://p.dw.com/p/4fdBX
Kenya | Ambaliyar Ruwa | Asarar Rayuka | Zaman Makoki
Ambaliyar ruwa ta yi mummnar barna a kasar KenyaHoto: Brian Inganga/AP/picture allinace

Shugaba William Ruto ya ce za a gudanar da dashen bishiyoyi na kasa a ranar, domin taimakawa wajen yaki da dumama ko kuma sauyin yanayi da kuma tuni da wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar. Haka kuma ya bayyana cewa za a bude makarantun kasar, bayan da aka samu tsaiko na tsawon makonni biyu sakamakon mamakon ruwan sama. Kenya da wasu kasashe na yankin gabashin Afirka sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, wadda ta tilasta sama da mutane dubu 235 suka kauracewa gidajensu tare da neman mafaka a tantuna.